Kanwar maza Hausa Novel
Kanwar maza Hausa Novel domin masu karatun novels a kyauta, asha karatu lahiya.
Takawa ne yayi sallama, ya shigo hankalinsa a kan iman, ya ƙarasa gaban gadon ta.
Nusaiba ta ce "Maman sabir, yaushe ki ka zo?"
"Tun ɗazu muka zo ni da mai sunan baba, ashe wannan ne yake jinyarta, ya tafi ya barta ita kaɗai" tayi maganar tana nuna Adam.
Nusaiba ta ce "Eyya, ni ce tare da ita, jininta na tafi kai wa a gwada, ba yadda zan yi ne shiyasa na tafi na bar ta".
Rumaisa ta ce "Au na zata shi ne ai".
Ta ƙarasa ta leƙa fuskar iman ta ce "Anty Iman ya jiki?".
Cikin ƙarfin hali ta ce "Da sauƙi Alhamdilillah ".
Adam ma lallaɓata yake yi, ko za ta ci wani abun, amma ta ce ita ba ta cin komai, ya din ga rarrashin ta, ta ce tuffa take so, takawa ya tashi ya ce bari ya je ya duba, ya sayo mata.
Daga mai sunan baba har Adam babu wanda ya kula wani, takawa na tafiya, iman ta fara ƙoƙarin kwanciya, mai sunan baba ya kalli Nusaiba ya ce "Ke, zuba mata abincin nan" gaba ɗaya suka tsaya suna kallonsa.
Rumaisa ta jinjinawa Nusaiba kai, dan ba ruwansa da baƙunta yanzu sai ya balebalesu da masifa.
Kanwar Maza Hausa Novel 1
Romon kifi ne da dankalin turawa, sai ƙamshi yake yi, idon iman ya cika da hawaye, dan ko ƙamshin abinci ba ta so, ya karɓa ya je gaban iman ya ajiye shi, ya tsaya mata ƙiƙam a ka, ba tare da ya furta komai ba, ta kama cokali, ta fara cin abincin nan, jikinta yana rawa, saboda tsoro da fargaba, ga wata irin Muguwar kunya, dan ba ta saba cin abinci a gaban maza ba, ko a taron mata ba iya ci take ba.
Sai da ta ci sosai sannan cikin faɗa ya ce "Kuna sane kuke wahalar da iyayenku, dan kun ga suna ta taku. Ke kuma tashi mu tafi" yayi maganar yana kallon rumaisa.
Ta tashi, kamar ta tuntsire da dariya, daga Nusaiban har iman ɗin kamar ka ce kyet su zura da gudu, saboda tsoro.
Ruma ta ce "Anty iman, Allah ya ƙara afuwa".
Cikin sanyin jiki ta ce "Amin maman sabir na gode".
Bayan tafiyarsu Nusaiba ta ce "Ke iman, wannan jarabbaben mutumin fa?"
"Yayan rumaisa ne" ta bata amsa.
Kanwar Maza Hausa Novel Part 2
"Kam bala'i, yau na ga wanda ya taka takawa iya tsare gida, daga zuwa ya hau ni da masifa"
Iman ta sunkuyar da kai ta ce "Mhmm, baki ga komai ba"
Babu daɗewa takawa ya dawo da tuffa, Nusaiba ta bashi labarin abun da ya faru, bai ce komai ba yayi shiru, dan shi kansa jin kan mai sunan baba yana bashi mamaki.
***
Iman jikinta yayi sauƙi, mama ma ta je asibitin ta dubata, ta warware, sai dai lokaci lokaci, kan ya kan matsa mata da ciwo, aka sallameta daga asibiti. Sai dai tun da ta koma gida, washegari ta sake tashi da ciwon kan, sai dai ta yi ƙoƙari ta jure, saboda ba ta san sanya ammi a damuwa.
A ranar da aka sallameta daga asibiti ranar Jabir ya dira Nigeria, daga wurin duba mahaifinsa.
Hajiya Lubabatu ta yi mamakin ganinsa ya dawo, dan sun yi da shi zai yi sati uku a can kan ya dawo.
"Wai kai Jabir, menene ya dawo da kai tun a yanzu?"
"Bakomai, ji na yi an ce iman babu lafiya, shiyasa na dawo ita ma na dubata".
Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Iman ɗin, kai a wa? Meye haɗinka da ita?"
"Bakomai zumunci kawai".
"Ban gane zumunci ba? Jabir kar na zo na ji wata magana saɓanin wadda nake son ji, ka san halina dai ban da kyau"
"Babu wata magana da zaki ji, kawai dai ina yi ne saboda Adam" tsaki tayi, ta shiga wata sabgar daban ta ƙyaleshi.
***
Yau tun da safe ammi ta kira mama, ta sanar mata da Adam zai zo wurin rumaisa, domin idan da wani abu da take buƙata ta gaya masa na game da shirin biki.
Amma mama ta ce "A'a hajiya, a ƙyaleta kawai, duk abun da aka yi Allah ya amfana"
Ammi ta ce "Ai da ni da ke, babu ruwanmu, namu ido abu ne na ma'aurata, dan haka yakamata su din ga tattaunawa domin su fahimci junansu!.
Kanwar Maza Hausa Novel Part 2
Sororo ta yi tana kallon sa, sam ba ta fuskanci in da ya dosa ba, abun da ta iya ganewa kawai shine ƙwaila, wato wadda ba ta da nono.
"Am talking to you kin tsaya kina kallona"
Cikin tsuke fuska ta ƙarasa gaban booth ɗin, manyan ledoji ne a ciki.
Ya dubeta ya ce "Gasu nan, iman ta ce yadin wanda zaki rabawa ƙawayenki, sauran bayanin ban riƙe ba, idan kun yi waya ta yi miki.
Akwai invitations da wurin da za ayi events, sai kayan sawarki".
Maimakon ta ce Ta gode, sai cewa ta yi "Ni ta yaya zan iya ɗaukar wannan kayan masu nauyi, kuma fa an sai mini kaya a gida, nifa kar ka zo daga baya ka din ga yi mini gori, idan ka san ba da zuciya ɗaya ka bani ba, ka riƙe abunka, ƙawayena za su saka abun da suke da shi" ɗagowa yayi ya kalli rumaisa, sai dai maimakon ya ji haushin abun da ta faɗa, sai ma ya yaba da yadda take taka tsan-tsan, ita dai kar ayi mata gori, tana da gudun abun wani.
Amma a zahiri, sauke mata kayan ya yi a ƙasa, ya rufe booth ɗin motarsa, ya saka hannu ya ɗauko wata babbar ledar a motarsa, ɗora mata a kan kayanta ya ce "Idan da wani abun ki saka Aliyu ya kirani" daga haka ya shiga mota ya ja ya tafi.
Gida ta shige ta ce wa su Huzaifa su je waje su kwaso kaya, idan ba haka ba a sace. Sun zata da wasa take yi, ashe da gaske take.
Gwaggo tuni ta zo kano, ita da lawisa, da zaliha, aka baje kayan da takawa ya kawo wa rumaisa.
Iya leshin da zata saka na dinner, ka san ba ƙarami bane ba, an ɗinka shi da jakarsa da takalmi da komai, an haɗo mata kayan fitar biki, ga kuma invitations, rumaisa ta yi ta kallon invitation ɗin tana mamakin wai sunanta ne a jiki.
Ledar nan da ya bata kuwa, babbar envelope ce a ciki wata dubu ɗari biyar ɗin ce a ciki.
Mama ta kalleta ta ce "Rumaisa tambayarsa ki ka yi?"
"Haba mama, to ni ce masa ma na yi, idan ya san zai yi mini gori wataran, ya ɗauki kayansa, ni za a sai mini a gida".
Gwaggo ta yi salati ta ce "Shi mijin naki ki ka gayawa hakan?"
Rumaisa ta ce "Mijina kuma taɓ".
Usman ya ce "Ke fa banza ce, yanzu ya kawo miki wannan uban kayan ki kasa yi masa godiya, saboda ke dai baki da alƙibla?"
Ta yi shiru tana muzurai. "Bari Aliyu ya dawo, ya kira shi a waya, ki yi masa godiya tun da ba ke ki ka nema masa kuɗin ba"
Haɗe rai ta yi, saboda zuwa yanzu yaya usy yana takura mata a kan mutumin fiye da kima.
Can kuma ta hau murna, tana lissafin ƙawayenta da zata bawa ankon da zasu ɗinka, ga uban kuɗi kuma tana gani.
Mama dai shiru tayi tana bin kayan da kuɗin da kallo, ita ba tarin kayan alatun ba, fatan ta Allah ya sa rumaisa ta shiga a sa'a ya sanya mata albarka.
***
Bin invitations ɗin yake da kallo, yana tuna lokacin da yayi auren fari, tun saura wata guda biki ya fara ɗoki, yana murna yana rabon invitation card, a wannan karon da shi da amaryar bai san wanda ya fi wani anti serious ba.
Rumaisa Mahmud, ya din ga kallon sunan nata, da kuma nasa Adam Sharif Galadima.
Bashir ne yayi sallama a falon, Adam ya amsa masa, ya ƙarasa suka gaisa sannan ya zauna ya kalli Adam ya ce "An kammala komai na gidan, zasu iya kai kaya a kowane lokaci".
Adam ya ce "Masha Allah, that's good ina godiya sosai, ina sidi?"
"Na ajiye shi, shima ya sha aiki ya gaji"
"Na gode sosai bashir, zan shiga na je na gani, daga nan sai na ɗauki ko mutum biyu a yayyenta, mu je su ga gidan".
Bashir ya ce "Hakan yayi, Allah ya sanya albarka, amma haryanzu fa ba ka fara rabon invitation ba, ko a social media ba a saka ba".
Adam ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Wallahi Bashir sam bana ɗokin auren nan, bana son duniya ma ta san zan yi shi, ni da za a shafa fatiha ma ba wannan events ɗin da na so hakan, rainon yarinya kawai za a kawo mini"
Bashir ya yi murmushi ya ce "Ka yi haƙuri, ammi ba zata zaɓa maka abun da zai cutar da kai ba. Sannan ba zai yiwu ka ɓoyewa duniya zaka yi aure ba, idan ta fasu aka sani, za a iya yi maka wani sharrin"
"Haka ne, haka zalika idan aka ga Yarinyar da zan aura, shi ma ba zan tsira ba, mussaman idan aka san ita ta zo da ɗa na daga hannun ƴan bindiga".
Bashir ya ce "Mafita ɗaya ce, duk yadda zaka yi ka ɓoye wa duniya cewar ba son auren ka ke yi ba, dole a ga farinciki da ɗoki a fuskarka".
Adam ya yi murmushi ya ce "Yadda za a ji daɗin cewa, saboda na auri yarinya ƙarama na kashe matata ko?"
"Ai dama dole sai an faɗi wani abu, amma yafi ace ka yi amfani da ƙaramar yarinya ka ɓoye wa duniya laifinka, na kai kashe matarka, ka turasasata ta aureka, dan kar a cigaba da surutu da zargin ya za ayi yarinya ƙarama kamarta ta kuɓuta da jariri a hannun 'yan bindiga"
Adam ya yi ajiyar zuciya, ya ɗan murza goshinsa ya ce "Duniya gidan rikici, Allah ya iya mana".
"Amin ya Allah"
Wayar takawa ce ta fara ringing, ya ɗauka ya duba ya ga sunan Aliyu.
Ya ɗaga ya saka a kunnensa tare da yin sallama, Aliyu ya amsa ya ce "Barka da wannan lokaci, ya hidima?".
"Alhamdilillah, ya taku hidimar?"
"Mun gode Allah, dama rumaisa ce za ta yi magana da kai"
Adam ya ce "Ok, ba ta".
Rumaisa ta karɓi wayar, Usman ya sakata a gaba ya tsareta da ido.
Ta karɓi wayar ta saka a kunneta, amma ta tsaya tana kallon Usman, ta kasa magana.
Ya daki ƙafarta ya ce "Ba zaki gaishe shi ba?"
"Ina wuni?"
Maimakon ya amsa ya ce "Ya aka yi?"
"Gaisheka fa na yi" ta yi maganar a ƙule.
"Ba a yi wa basarake irin wannan gaisuwar, babu ladabi a gaisuwarki, dan haka ko sau nawa zaki yi ba zan amsa ba, riƙe kayarki, ina jin ki"
Rumaisa ji ta yi kamar ta yi zagi, meye aibun gaisuwar ta, idan ba neman bala'i ba.
"Idan kin shirya yin magana, sai ki sake kirana".
"Su yaya ne suka ce dole sai na kiraka na yi maka godiya, na gode, kuma wai kuɗin da ka bani sun yi yawa, sannan......"
Kanwar Maza Hausa Novel Part 3
"Lokacin da ki ka san abu yakamata, ba sai wani ya saka ki ba, sai ki neme ni, yayyenki na ƙoƙari wurin baki tarbiyya, Allah ya biya su, kuɗi kuma ki zubar" ya kashe wayarsa.
Dungurar da wayar ta yi a ƙufule, ta ce "Yaya usy kalli abun da ka janyo mini"
Dungure mata kai yayi ya ce "Ki ka jawa kanki dai, ke a rayuwar duniya baki iya siyasa ba? Ji yadda ki ke gantsara masa magana, kamar kashi ba tausasa lafazi, ba ɗan karya murya, wai ke ma namiji ce irinmu ne? to ko mu muna kashe murya, ranar da na kama malam habu yana waya, kamar ma nutse dan kunya, amma ke kina ta wani shirme.
Ke, tashi mu je ɗaki, na yi miki bayanin me auren ya ƙunsa, in fayyace miki komai in gaya miki, na ga mama ba ta da niyyar gaya miki, daga ita har su gwaggon.
Aliyu ya ce "Kai fa wasu lokutan baka da kamun kai, uban me zaka gaya mata?".
"Komai ma gaya mata zan yi, yo haka za ta je ta zauna masa a gida kamar gardi, idan ka ga tana tausa murya to wani abun take nema, tashi mu je na fayyace biri har wutsiya".
Aliyu da dariya ta ƙwace masa ya ce "Mama, wallahi usman ya zama abun da ya zama, zai juyawa yarinya tunani, saboda bashi da kamun kai".
Usman ya ce "Eh, bani da kamun kan, ni ina ma ni za ayi wa auren nan, wai muna zaune ƴar da aka haifa a gabanmu za ta rigamu girma Allahu Akbar wata shekarar sai ta fara ƴa ƴa kuma".
Aliyu ya ce "Wani irin ta fara ƴaƴa wata shekarar, kamar wata bishiyar lemo, wannan yarinyar ko nan da shekara biyar albarka"
Wani irin kallo Usman ya yi masa ya ce "Haba, a banza za ku kaita ya din ga bata abinci, yana biya mata kuɗin makaranta ko? You don't get sense. Ko kaza dan a cinyeta ake killace ta a sai mata dusa, kar ka yaudari kan ka".
Aliyu ya ce "kai haba, she's too young for it, and the man is very decent and calm, bana tunanin haka".
Usman ya yi dariya ya ce "Uban calm da decent ɗin, that thing don't get sense, don't fool yourself, if not ku fasa aurar da ita, hauka ake mutum zai kashe kuɗi ya auri ƴa ya sakata a gaba yana kallonta, Allah ya sa jaririya ce"
Aliyu ya yi tsaki ya ce "Zaka ɓata mini rai "
Rumaisa da ba gane kan hirar take ba, ta din ga bin su da kallo, Usman ya ce "To Algume, sai kallon bakinmu ki ke, ƙila kin san komai, ki ka yi wani kasaƙe da kai".
Aliyu ya ce "A hakan ta san komai? Tana wannan gidadancin".
Usman ya ce "Kuma fa haka ne, to jeki na fasa gaya miki komai, duniya zata gaya miki, Allah ya shiryeki".
"Nuraini, Allah ya baka abun yi na aurara da kai, ina ga daga rumaisa kuma sai kai, tun baka wuce in da nake tunani ba" a guje Usman ya faɗa ɗakinsu, dan sam bai san mama ta ji hirarsu ba.
Kanwar Maza Hausa Novel Part 3
***
Jabir ya din ga juya invitation ɗin, sannan ya kalli Adam ya ce " da gaske Adam saura kwanaki a ɗaura maka aure, amma ban sani ba?"
"Am sorry, abun ne ya zo cikin gahgawar gaske fiye da yadda na yi zato, sai haƙuri".
Jabir ya sake kallon invitation ɗin, sannan ya ce "To ita kuma wacece, a ina take? Kamar na san sunan nan".
Adam ya ce "Zaka ganta very soon".
"Da jamil ya gaya mini maganar auren nan, na zaci da wasa yake yi, ashe da gaske ne, Allah sarki samha ina tausayin yarinyar nan sosai".
Adam ya ce "Please, don't raise that issue here, ku daina ganin laifina, ƙaddara ce ta zo a haka".
Jabir ya ce "Na yadda, ban ce wani abu ba, kawai dai ina jin tausayinta ne, sai dai na yi mamakin yadda har ka nemi aure, har ka samu ban sani ba, yaushe muka fara haka da kai".
"Jabir, this is an arranged marriage,
Kanwar maza Hausa Novel last section abinda zamu iya kawowa kenan mun gode.



0 Comments